‘Ba haka kawai na bayar da umarnin kama Abba Kabir Yusuf ba’ – Uwargidan DG SSS, Aisha Bichi

0 336

Aisha Bichi, uwargidan babban daraktan hukumar tsaron farin kaya ta SSS, Yusuf Bichi, ta bayar da umarnin kama dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, tare da hana shi shiga jirgin Air Peace daga Kano zuwa Abuja a daren Lahadi.

An rawaito cewa rikicin ya fara ne a kofar wajen zaman manyan mutane na filin jirgin saman Mallam Aminu Kano da ke Kano a lokacin da ayarin motocin dan siyasar suka jawo cunkoson ababen hawa, wanda ya kawo tsaiko ga ayarin motocin Aisha Bichi.

Majiyoyi sun ce lamarin ya fusata Aisha Bichi yayin da jami’an tsaronta suka fara lakadawa mutane duka tare da bugun motoci.

An rawaito cewa lamarin ya kara ta’azzara ne a lokacin da ta hango wani dan tawagar ‘yan siyasar, mai suna Garba Kilo, yana daukar hoton lamarin da wayarsa.

Shaidu sun ce yayin da kura ta fara lafa, dan takarar jam’iyyar NNPP ya shiga wajen zaman manyan mutane domin ganawa da ita, kasancewarta kawar matarsa, kuma ya koka kan halin rashin da’a na ma’aikatan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: