Fadar shugaban Kasa ta ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaban kasa Bola Tinubu na shugabancin ƙasar, muƙamin da ɗantakarar jam’iyyar PDPn yake ta famar nema har sau shida amma bai yi nasara ba.
Fadar shugaban kasar ta soki Atikun ne saboda shawarar da ya bayar ta sauye-sauyen tattalin arziƙi da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa a wani saƙo da ya wallafa a shafin Tweeter da ya sanya kwanan nan.
Wani saƙo da ya fito daga fadar shugaban ƙasar, wanda mai ba shugaban shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, ya ce, tun bayan da Atiku ya sha kaye a zaɓen 2023 a hannun Tinubu, ya fi mayar da hankali kan zagon-ƙasa ga Shugaba Bola Tinubu maimakon mayar da hankali kan matsalolin jam’iyyarsa. Sanarwar ta ƙara da cewa maganganu da shawarwarin da Atiku yake bayarwa a kan tattalin arziƙi sun nuna tsananin rashin fahimtarsa da ainahin halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.