Atiku da Peter Obi sun caccaki fadar shugaban kasa kan kin amincewa da rahoton EU kan zaben shugaban kasa

0 548

‘Yan takarar shugaban kasa na jam’yyar PDP da LP a zaben 2023, Atiku Abubakar da takwaransa Peter Obi, sun caccaki fadar shugaban kasa kan kin amincewa da rahoton karshe na kungiyar tarayyar turai kan zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tawagar masu sa ido ta ƙungiyar Tarayyar Turai a cikin rahotonta ta caccaki sakamakon zaɓen da rashin tsari.

Sakamakon zaben dai ya sha takun-saka tsakanin jam’iyyun PDP da LP da ‘yan takararsu da suka yi zargin cewa zaben bai dace ba.

Babban jami’in sa ido na tawagar ƙungiyar Tarayyar Turai, Barry Andrews, ya yi jawabi ga manema labarai a makon da ya gabata, inda ya bayyana cewa zaben ya gaza daga tsarin da aka tsara, don haka ya nuna bukatar kara yin garambawul na doka da na aiki domin fito da gaskiya, hada kai, da rikon amana. Ya ce gazawar da aka samu a cikin dokar zabe na 2022, ya kawo cikas wajen gudanar da sahihin zabe tare da rusa amanar da aka bawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: