Asusun lamuni na duniya IMF, ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta mai da hankali kan matsalar karancin abinci a kasar

0 278

Asusun lamuni na duniya IMF, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta mai da hankali kan matsalar karancin abinci a kasarnan.

Kalaman na IMF na zuwa ne a ranar da gwamnoni suka ce dole ne Najeriya ta fara sarrafa kaya a cikin gida musamman a bangaren abinci idan har ana so jama’a su fita daga cikin kuncin rayuwa.

A wani taron shekara-shekara na Shugabanci da bada lambar yabo, IMF ta bayyana matsayinta a cikin sanarwar da ta fitar wadda ta aikewa kasar nan.

Haka ma dai tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, wanda ya koka kan wahalar da kasar ke ciki, ya ce ba wai yana burin zama shugaban kasa ne kadai ba amma yana fatan yiwa Najeriya aiki.

Sai dai kuma shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri, yana mai ba su tabbacin cewa garambawul din tattalin arzikin kasar nan zai haifar da sakamako mai kyau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: