Asusun adashen gata na yan fansho yana da jimillar dukiyar naira biliyan 17 a jihar Jigawa

0 204

Sakataren zartarwa na hukumar asusun adashen gata na fansho na jiha da kananan hukumomin Jigawa, Alhaji Hashim Ahmed Fagam, ya ce asusun yana da jimillar dukiyar naira biliyan 17.

Babban sakataren ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga hukumar fansho ta jihar Kano wadanda ke ziyarar koyon aiki a jihar Jigawa.

Hashim Fagam ya ce nan ba da jimawa ba asusun zai biya kudi naira biliyan 1 da miliyan 200 ga ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da iyalan wadanda suka mutu a jiharnan.

Da yake magana tunda farko, mamba na dindindin a kwamitin amintattu na asusun fansho na jihar Kano, Alhaji Maifada Bello Kibiya ya ce tawagar tazo jihar Jigawa ne don koyo daga tsarin fansho na jihar da nufin magance wasu matsaloli da kalubalen da ke tattare da tsarin biyan fansho a jihar Kano.

Bello Kibiya wanda ya bayyana tsaran fansho na jihar Jigawa a matsayin mafi kyau a kasarnan, ya ce tawagar za ta gabatar da sakamakon bincikenta ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje domin amincewarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: