APC ta shawarci Sanata Ali Ndume kan ya riƙa gabatar da ƙorafin sa kai tsaye ga Bola Tinubu

0 157

Jam’iyyar APC mai mulki ta shawarci tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume kan ya riƙa gabatar da ƙorafin sa kai tsaye ga shugaba Bola Tinubu, a madadin fita fili yana sukar tsare-tsaren gwamnatin a bainar jama’a.

A wata hira da jaridar PUNCH darakatan yaɗa labaran jam’iyyar APC na ƙasa, Bala Ibrahim ya ce kowanne ɗan ƙasa yana da ƴancin bayyana ra’ayin sa a tsarin dimokuraɗiyya, amma akwai buƙatar manyan ƴan siyasa irin su Ndume su riƙa kiyaye irin bayanan da zasu yi a bainar jama’a.

Sanata Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a majalisar dattawan ya bayyana a cikin shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa, inda ya buƙaci gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauki matakan kawo sauƙin halin matsi da ƴan Najeriya ke ciki, ya yi kiran a dakatar da ƙarin farashin mai a ƙasa.

Sanata Ndume ya kuma fitar da wata sanarwa ga manema labarai domin jaddada matsayar sa a kan halin da ake ciki, inda ya yi iƙirarin cewa akwai wasu da ke tunzura gwamnati tana aiwatar da tsare-tsare masu tsauri.

A watannin baya ma jam’iyyar APC ta nemi majalisar dattawa ta ladabtar da Sanata Ndume ta hanyar ƙwace mukamin sa na mai tsawatarwa saboda yadda ya ke fita kafafen yaɗa labarai yana sukar gwamnatin APC. Daga baya sanatan ya nemi afuwa kuma jam’iyyar ta yafe masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: