APC Ta Kafa Kwamiti Domin Bincikar Sanata Bulus da Yunusa Ahmad.

0 195

A jiya ne jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta kafa wani kwamiti da zai binciki Sanata Bulus Amos da dan majalisar wakilai, Yunusa Ahmad Abubakar, bisa zargin yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Da yake zantawa da manema labarai jiya a garin Lubo da ke karamar hukumar Yamaltu/Deba, sakataren jam’iyyar APC na mazabar Lubo/Difa/Kinafa, Samaila Ali, ya ce jam’iyyar na zargin cewa dan majalisar, Yunusa Abubakar ya hada baki da wata jam’iyyar adawa a lokacin zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a jihar.

Ya ce suna sane da cewa dan majalisar tarayyar ya umurci sauran ‘ya’yan jam’iyyar da magoya bayansa da su zabi wata jam’iyyar da ba APC ba. Har ila yau, shugaban jam’iyyar APC na mazabar garin Bambam na karamar hukumar Balanga a jihar, Muhamamdu Kaka, ya ce shugabannin jam’iyyar na yankin sun kafa kwamitin mutum biyar da zai binciki Sanata mai wakiltar Gombe ta Kudu, Bulus Amos, bisa zarginsa da yi wa jam’iyyar zagon kasa a lokacin zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: