APC ta buƙaci Fubara ya yi murabus ko a tsige shi

0 48

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Rivers, Tony Okocha ya yi kira ga Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulkin jihar, ko kuma a tsige shi.

Okocha ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ƴanmajalisar jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi.

“Hukuncin kotun ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tun da farko, bayan hukuncin kotun ƙolin, majalisar jihar ta ba gwamnan jihar wa’adin kwana biyu ya sake gabatar da kasafin kuɗi, gayyatar da ya ƙi amsawa.

Daga baya shi kuma ya gayyace su gidan gwamnati domin su tattauna, inda su ma suka ce ba za su je ba, domin a kafofin sadarwa suka ga gayyatar.

– BBC Hausa

Leave a Reply