Anyi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba

0 373

Hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a fadin kasarnan daga yau zuwa ranar Laraba.

Rahoton hasashen yanayin hukumar wanda aka saki a Abuja, yayi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a yankin Arewa da ya kunshi jihoshin Kaduna, Jigawa, Kebbi, Sokoto, Gombe, Bauchi, Yobe, Adamawa, Taraba da Borno, a yau da dare.

Haka kuma Hukumar ta yi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a jihoshi Taraba, Kebbi, Sokoto da Zamfara, gobe da safe. Kazalika ta yi hasashen samun ruwan sama da tsawa a jihoshin Borno, Kano, Kaduna, Taraba, Adamawa, da Bauchi, a yammacin gobe.

Kazalika Hukumar ta yi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a jihoshin Taraba, Adamawa, Kaduna, Bauchi, Kebbi da Gombe a ranar Laraba da safe.

Hukumar ta kuma yi hasashen samun ruwan sama hade da tsawa a jihoshin Borno, Zamfara, Sokoto, Yobe, Jigawa, Kano, Kaduna, Taraba, da Bauchi, a yammacin ranar ta Laraba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: