Anyi asarar dukiya ta miliyoyin nairori a gobarar da ta tashi a Helkwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa
An samu asarar dukiya ta miliyoyin nairori a yau sakamakon gobarar da ta tashi a Helkwatar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa da ke kan titin Broad Street a Legas.
An ce gobarar ta tashi ne sanadiyar matsalar wutar lantarki kuma ta shafi ofisoshi uku a hawa na 6 na ginin amma ba a rasa rai ba.
Wasu ma’aikatan hukumar, wadanda suka nemi a sakaya sunan su, sun ce suna shirin fara aikine lokacin da gobarar ta tashi.
Ma’aikatan sun ce an nemi wadanda ke kan benen da abin ya shafa su kasance a wani waje a kasa inda jami’an tsaro suka dauki adadin wadanda ke bakin aiki.
Babban Manajan Sadarwa na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa, Olaseni Alakija, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce jami’an sashen kashe gobara na hukumar sun gaggauta zuwa wajen da abin ya faru suka shawo kan gobarar.
Idan za a iya tunawa dai, an yi asarar dukiyar da ta kai biliyoyin nairori lokacin da ‘yan daba suka kona Helkwatar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta kasa yayin zanga-zangar EndSARS.