Jam’iyyar PDP zata zabi dan takararta na shugaban kasa daga yankin Arewa domin zaben 2023

0 156

Akwai kyakykyawan zaton cewa jam’iyyar PDP zata zabi dan takararta na shugaban kasa domin zaben 2023 daga Arewacin kasarnan, kasancewar masu ruwa da tsaki na shirin mika shugabancin jam’iyyar ga yankin Kudu.

A lokacin zaman kwamitin gudanar jam’iyyar a karshen mako, jam’iyyar ta sanar da cewa zata fitar da tsarin karba-karba domin shugabannin jam’iyyar, a zaman kwamitin da aka shirya gudanarwa daga ranar 30 zuwa 31 ga watan Oktoba.

Ana cigaba da shirye-shiryen zaben sabbin shugabannin jam’iyyar, duk da kasancewar ana fama da dambaruwar siyasa a jam’iyyar wacce ta haifar da kararraki a kotuna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: