Ana zargin wani mai sayar da Yalo da yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara tara

0 350

Ana zargin wani mai sayar da Yalo mai suna Auwalu Abubakar a karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano da yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara tara.

Lamarin ya faru a ranar 9 ga watan Nuwamba, inda rahotanni suka bayyna cewa sai da aka kwantar da yarinyar har tsawon mako guda kafin daga bisani a sallame ta daga asibitin ’yan sanda da ke Bompai, Kano.

Da take magana kan laifin, ‘yar uwar yarinyar, Aisha Auwal, ta ce, “An fara dawo da ita gida tana kuka bayan an dawowarta daga makaranta inda tace ta fada cikin magudanar ruwa kuma ta samu raunuka.

Ta kara da cewa daga bisani ne suka gano abin da ya faru da ita bayan sun garzaya da ita asibitin kwararru na Murtala Muhammed inda aka tabbatar da anyi mata fyade.

Ta ci gaba da cewa, “bayan gano wanda yayi mata wannan aika aika mai suna Auwalu wanda ke sayar da Yalo,  tuni ‘yan sanda sun kama shi.

Sai dai da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba. Majiyoyi sun ce yarinyar marainiya ce, don haka an yi kira ga hukumomi da su tabbatar an hukunta wanda ya aikata laifin

Leave a Reply

%d bloggers like this: