Ana Zargin Rarara Da Rashin Biyan Bashin Wayoyin Salula Daya Kai Naira 10,300,000

0 174

Babbar kotun shariar musuluci dake zama a rijiyar zaki karkashin mai sharia Halhalatul Khuza’i Zakariyya ta bada umarnin sake mika sammaci ga mawaki Dauda Kahutu Rarara, bida rashin halartar zaman kotu.
Ana zargin Rarara da rashin biyan kudaden waya da ya kai naira miliyan 10 da dubu 300, wanda ya karba daga hannun wani dan kasuwa Muhammad Ma’aji sannan ya rabawa mutane.
Lauyan mai kara Barr I. Imam ya sanar da kotu cewa wanda ake zargin bai mutunta umarnin kotu ba, dan haka ya roki kotun da ta da a kamoshi.
Haka kuma Imam ya sanar da kotun cewa ba lallai takardar sammacin ta samu wanda ake zargin ba.
Kotun ta tambayi maga takardarta Ismail Zuhudu ko ya kai takardar sammacin da kotu ba bashi, ya kuma tabbatarwa kotun cewa manna takardar a kofar gidan wanda ake zargin, kamar yadda kotu ta bayar da umarni, saboda duk kokarin sa na haduwa dashi yaci tura.
Mai sharia Halhalatul Khuza’i Zakariyya yace, kasancewar wannan shine karon farko da yaki amsa gayyatar kotun, dan haka ta dage sauraron karar zuwa jibi 13 ga watan Afrilu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: