Ana tsammanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci daurin auren dansa, Yusif da Zahra Bayero

0 357

Ana Tsammanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci daurin Auren dansa Yusif wanda zai Auri Zahra Bayero a gobe Juma’a, A cewar Shugaban Kwamatin Tsare-Tsaren Shehu Ahmed, kamar yadda ya fadawa manema labarai.

Shehu Ahmed ya ce Manyan Baki ne daga ciki da wajen Jihar Kano ake saran zasu halarci Daurin Auren wanda aka tsara za’a gudanar a babban masallacin Jumu’a na Bichi da karfe 1:30 na ranar Jumu’a.

An gano cewa Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Asabar zai mika Sanda ga Sirikin Yusuf Buhari, kuma Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Madakin Bichi, Alhaji Nura Shehu Ahmad, wanda shine shugaban kwamitin shirye-shirye na bikin auren da kuma naɗin Alhaji Nasir Ado Bayero.

Tuni aka girke Jami’an tsaro a ciki da wajen birnin Kano musamman Bichi, wanda suka haɗa da, yan sandan farin kaya (DSS), Jami’an hukumar Civil Defence, da yan Hisbah, da kuma yan Bijilanti.

Haka kuma ya ce tuni aka shirya Kwamatoci domin tabbatar da cewa anyi bukukuwan Cikin Nasara.

Kazalika, Alhaji Ahmad yace an girke Jami’an tsaro a filin Sauka da tashin Jirage na Malam Aminu Kano zuwa garin Bichi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: