Ana samun ƙaruwar kamuwa da cutar kwalara a najerya yayin da damina ke ƙara kamari-NCDC

0 104

Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar da sanarwar fadakar da jama’a game da ƙaruwar kamuwa da cutar kwalara a fadin kasar yayin da damina ke ƙara kamari.

An samu rahoton bullar cutar a jihar Legas a baya-bayan nan, lamarin da ya ƙara dagula al’amura.

Daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Yunin 2024, an samu jimillar mutum 1,141 da ake zargi da kamuwa da cutar kwalara da kuma 65 da aka tabbatar sun kamu da cutar, kuma mutum 30 sun ne suka mutu duk daga ƙananan hukumomi 96 a faɗin jihohi 30 sakamakon cutar. Jihohin da suka fi fama da cutar, waɗanda ke bayar da kashi 90% na yaɗuwar cutar sun hada da Bayelsa da Zamfara da Abia da Cross River da Bauchi da Delta da Katsina da Imo da Nasarawa da kuma Legas

Leave a Reply

%d bloggers like this: