Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2023 a ranar Talata, 3 ga Janairu, 2023.
Dan majalisar ya bayyana haka ne a jiya bayan ziyarar da ya kai wa shugaban kasar a ofishin sa.
Ya shaida wa manema labarai na fadar shugaban kasa cewa, ya yi wa shugaban kasa bayanin yadda aka zartar da kudurin kasafin kudin, wanda ya kunshi kudaden babban zabe da sauran batutuwan da suka shafi kasa.
Ya kara da cewa majalisar dokokin kasar nan na fatan amincewar shugaban kasa akan kasafin a ranar aiki ta farko ta sabuwar shekara.
Lawan ya bayyana cewa, jinkirin da aka samu wajen zartar da kudirin ya biyo bayan wasu kura-kurai ne a alkaluman da aka gabatar wa majalissa tunda farko.
A cikin shekaru hudu da suka gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba sanya hannu kan kasafin kadi a sabuwar shekara ba sai a bana. Yana sanyawa ne gabanin karewar shekara.