Ana sa ran haifar yara akalla dubu 365,595 cikin shekarar 2023 a jihar Jigawa

0 297

Kwamishinan lafiya Dr. Abdullahi Kainuwa ne ya bayyana haka a taron bikin ranar kayyade iyali ta duniya ta bana, wanda aka gudanar a Dutse babban birnin jihar.

A wajen taron, Dokta Kainuwa ya ce matan da suka kai shekarun haihuwa a jihar suna karbar maganin kayyade iyali a akalla a cibiyoyin kiwon lafiya 300 daga cikin 761 da ake dasu jihar.

Ya ce daga cikin masu juna biyu Dubu 365,595 a bana, sama da dubu 273 sun haife a watan Yuli.

Dokta Kainuwa ya ce jihar Jigawa na da mata sama da miliyan 1,608,616 da suka kai shekarun haihuwa, kuma ma’aikatar ta yi shirin ganin nan da shekarar 2027, kashi 30 cikin 100 na matan suna samun maganin bayar da tazarar iyali na zamani.

An samu alkaluman adadin masu juna biyun ne daga cibiyoyin kiwon lafiya da suke ziyarta akafin haihuwa, da lokacin da kuma bayan haihuwa. Mai yiwuwa, adadi mai yawa na mata ba sa ziyartar cibiyoyin kiwon lafiya yayin da suke dauke da juna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: