Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce ana kan shirye-shiryen mika mulki ga zababbiyar gwamnati.
Boss Mustapha, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin mika mulki na shugaban kasa, ya bayar da wannan tabbacin a jiya a wani taron manema labarai da ya yi wa ‘yan jarida akan yadda ake tafiyar da shirye-shiryen mika mulkin tun bayan kaddamar da kwamitin.
A cewarsa, tsarin na tattaunawa da manema labarai ya zama dole ta yadda ‘yan Najeriya za su rika sanin abubuwan da ke faruwa, da shigar da jama’a cikin harkokin da kuma kafa ginshikin mika mulki cikin lumana a kasar.
Da yake amsa tambayoyi kan katsalandan da ka iya samuwa ta shari’ar da kotuna ke yi kan zaben, Boss Mustapha ya ce kararraki a kotuna ba za zu dakatar da shirin mika mulki ba. A ranar 14 ga watan Fabrairu ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mika mulki na mutane 22 na shugaban kasa gabanin mika mulki ga gwamnati mai jiran gado a shekarar 2023.