Ana kama kwamandan rundunar soji kan zargin sayar da janareto da motocin aiki ga ‘yan gwangwan

0 93

An tsare kwamandan runduna ta ‘3 Brigade Kano’, Birgediya Janar M.A. Sadiq, a dakin tsaro na rundunar ‘yansandan Sojoji da ke Abuja, bisa zargin karkatar da tallafin shinkafa, da sayar da kayan aikin soji da suka hada da janareto da motocin aiki, ga masu sana’ar gwangwan.

Wasu majiyoyin da suka zanta da jaridar DAILY NIGERIAN bisa sharadin sakaya sunansu sun ce, hedikwatar tsaro ta kasa ta bayar da shinkafar ne ga rundunar ta kasa baki daya domin raba wa sojoji a matsayin agajin gaggawa.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa, hedikwatar tsaro ta raba shinkafar a kalla sau uku ga sojojin kasar, kamar yadda aka tsara.

Janar din da aka kulle, a cewar majiyoyi, ya raba shinkafa mai nauyin 50kg sau daya maimakon sau Uku ga sojojin sannan ya sayar da sauran.

DAILY NIGERIA ta tabbatar da cewa, an maye gurbin wanda ake zargin da wani tsohon magatakarda na Kwalejin Tsaro ta kasa, Birgediya Janar A.M. Tukur.

Kakakin Rundunar Soji, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, bai amsa kira da sakon da aka tura masa ta wayar sa ba har lokacin hada wannan rahoto.

Leave a Reply

%d bloggers like this: