Ana gudanar da wasu tsare-tsare domin sauya ma’aikatar jin kai da yaki da fatara

0 196

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya na gudanar da wasu tsare-tsare domin sauya ma’aikatar jin kai da yaki da fatara ta kasa.

Muhammed Idris ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a taron tattaunawa na jaridar Aminiya karo na 21 a Abuja.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta na duba lamarin baya-bayan nan a ma’aikatar kula da jin kai don ganin an daidaita lamarin da kuma gujewa wa kuskure a nan gaba.

Dangane da cire tallafin man fetur, ministan, wanda ya ce babu wani tsari mai kyau da ke zuwa cikin sauki, ya kara da cewa gwamnati na kokarin magance kalubalen da ake samu sakamakon cire tallafin man fetur. A cewarsa, gwamnatocin jihohi da kungiyoyin kwadago suna sane da abin da gwamnatin tarayya ke yi na dakile illoli da kulubalen da ake fuskanta a dalilin cire tallafin man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: