Ana fuskantar aukuwar sabuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohi 11 na Najriya

0 166

Hukumar Kula Da Al’amuran Da Suka Shafi Yanayin Ruwa Ta Kasa (NIHSA), ta bayyana cewa ana fuskantar aukuwar sabuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar nan 11.

Hukumar wacce ta bayyana haka a ranar Laraba, ta ce sabuwar ambaliyar da ake fuskanta daga madatsar ruwa ta Lagdo ce da ke kasar Kamaru.

Babban daraktan hukumar, Umar Muhammed, ya ce mahukuntan kasar Kamaru sun sanar da cewa za su fara sakin ruwan dam din Lagdo, daga ranar Talata 17 ga Satumba, 2024.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “ana sa ran sakin ruwan da karfinsa zai karu zuwa mita 1000 cikin kowace dakika a cikin kwanaki bakwai masu zuwa, bisa la’akari da kwararar da yake yi daga kogin Garoua.

Kamar yadda bayanan hukumar suka nunar, jihohin da ke fuskantar wannan ibtila’i su ne: Adamawa, Taraba, Binuwai, Nasarawa, Kogi, Edo, Delta, Anambra, Bayelsa, Kuros Ribas, Ribas.

Hukumar ta NIHSA ta bukaci gwamnati a dukkan matakan gwamanatoci su kara fadakar da al’ummomin jihohin da abin ya shafa wajen bin matakan da suka dace, don rage hadarin aukuwar ambaliyar ruwan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: