Kungiyar da ke kula da ‘yan ci rani ta duniya ta ce ana fargabar mutum 61 sun rasa ransu bayan wani kwale kwale ya nitse a Libya.
Kungiyar ta rawaito wadanda suka tsira da ransu na cewa kwale kwalen na dauke da mutane 86 ne ciki har da mata da yara wadanda ke kan hanyarsu daga Libya zuwa turai.
Dubban mutane ne ke rasa rayukansu a yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa Italia inda yawancinsu kuma daga Tunisia ko Libya suka fito.
A bana kadai an yi hasashen cewa mutum fiye da 2,200 ne suka rasa ransu a yayin irin wannan tafiya.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa akasarin mutanen sun fito ne daga Najeriya da Gambia da sauran ƙasashen Afrika. Ya kuma ce sauran waɗanda aka ceto an garzaya da su wata cibiya da ake tsare su a Libya kuma suna ci gaba da karɓar taimakon magunguna.