Ana Cigaba Da Warkewa Daga Cutar Korona A Nijeriya

0 171

Yawan mutanen da suka kamu da coronavirus a Najeriya, jiya Alhamis da yamma, ya karu zuwa 184, bayan cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da sabbin mutane 10 da suka kamu da cutar.

Kamar yadda sabbin alakuman da cibiyar ta NCDC ta saki suka nuna, mutane 7 cikin sabbin wadanda suka kamu, suna Lagos, yayin da sauran ukun suke babban birnin tarayya.

Kawo yanzu Jumillar jihoshin 12 ne tare da babban birnin tarayya kwayar cutar ta bulla a nan Najeriya.

Cibiyar tace kawo karfe 8 na dare, jiya Alhamis, akwai mutane 184 da aka tabbatar sun kamu da Covid-19 a Najeriya.

Jumillar mutane 20 aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga kwayar cutar, yayin da ta hallaka mutane 2.

Leave a Reply

%d bloggers like this: