Ana cigaba da jaddada rigakafin cutar Corona saboda tsoron Omicron

0 147

Gwamnatin Tarayya ta amince a fara jaddada wa ‘yan ƙasar rigakafin cutar da aka yi musu tun farko, a daidai lokacin da kasashen Duniya suke fargabar bullar sabuwar Nau’in cutar Corona.

Shugaban hukumar lafiya a matakin farko na Kasa, Dr Faisal Shuaib, shi ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, yana mai cewa an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya da zummar tsaurara yaƙi da cutar.

Ya ce za a yi wa mutanen da tuni suka yi rigakafin sau biyu na samfurin AstraZeneca ko Moderna ko Pfizer Bio-N-Tech ko kuma waɗanda aka yi wa samfurin Johnson and Johnson sau ɗaya.

Sharaɗin da aka shimfiɗa na samun allurar shi ne sai mutum ya kai shekara 18 da haihuwa ko fiye, sannan sai mutum ya yi wata shida da yin allura ta biyu ta samfurin AstraZeneca ko Moderna ko Pfizer Bio-N-Tech, ko kuma tsawon wata biyu da yin Johnson and Johnson.

Za a fara gudanar da allurar ce daga ranar 10 ga watan Disamba a dukkan jihohin Najeriya, a cewar Dr Shuaib.

Gwamnati ta ɗauki matakin ne yayin da sabon nau’in korona na Omicron mai hatsari yake bazuwa a faɗin duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: