Ana cigaba da cece kuce biyo bayan samun rahoton da NBC ta bayar na umartar dukkan kafofin yaɗa labarai da su goge shafinsu na Twitter.
Ana cigaba da cece kuce biyo bayan samun rahoton da Hukumar Kula Kafofin Yaɗa Labarai a Najeriya ta National Broadcasting Commission (NBC) ta bayar na umartar dukkan kafofin yaɗa labarai da su goge shafinsu na Twitter nan take.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon haramta amfani da dandalin da gwamnatin ƙasar ta yi.
Hukumar ta umarci kafofin labarai da su goge shafukansu sannan su daina amfani da Twitter a matsayin hanyar samun labarai musamman a shirye-shiryen da ake buga waya.
Sanarwar da Farfesa Armstrong Idachaba ya sanya wa hannu ta ce Sashe na 2(1) na dokar NBC ya sharɗanta cewa hukumar na da haƙƙin tilasta bin dokar ƙasa da tsare-tsare.
Kazalika, sashe na 3.11.2. ya tanadi NBC ta tilasta aiwatar da doka a kowane lokaci a yanayin da aka tabbatar cewa doka da oda sun zarta aikata laifi da kuma hatsaniya.
Harammcin amfani da Twitter a Najeriya ya fara ne tun tsakar daren 5 ga watan Yuni bayan gwamnati ta zargi dandalin da “rura wutar rikici da raba kawunan ‘yan ƙasar.