Ana ci gaba da ayyukan ceto a ambaliyar da ta ɗaiɗaita yankin Valeancia

0 112

Ana ci gaba da ayyukan ceto a ambaliyar da ta ɗaiɗaita yankin Valeancia a ƙasar Sifaniya a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Zuwa yanzu dai waɗanda suka rasu sun kai aƙalla mutane 95, a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan ceto.

Daga cikin waɗanda suka rasu akwai ɗan Burtaniya mai shekaru 71 bayan an ceto shi a gidansa a garin Malaga.

Kawo yanzu dai ruwan ya tsagaita, amma firaiministan ƙasar Pedro Sanchez, ya ce akwai buƙatar mazauna yankin su ɗan dakata, a tabbatar da tsayawar ambaliyar. Hukumomi dai a ƙasar sun ce har yanzu ba a tantance haƙiƙanin mutane nawa suka ɓace ba a sanadiyar ambaliyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: