Tsoffin shugabannin Najeriya da na ƙasashe masu maƙwabtaka da sauran masu faɗa a -ji a ƙasar na birnin Abuja inda ake taron ƙaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Bikin wanda ya samu halartar tsoffin shugabannin Najeriya da suka haɗa da Janar Yakubu Gowon da janar Olusegun Obasanjo da Abdussalami Abubakar da kuma tsoffin shugabannin ƙasar Ghana, Nana Akufo Addo da na Sierra Leone Arnest Bai Koroma.
Littafin mai shafi fiye da 400 ya yi waiwaye kan rayuwar tsohon shugaban ƙasar daga yarintarsa a matsayin maraya har zuwa rayuwarsa ta makaranta da shigaa aikin soji.
Da yake yinbitar littafin, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce littafin ya yi cikakken bayani kan juyin mulkin soji da irin rawar da janar Ibrahim Babangidan ya taka.
A karon faro janar Babangida a cikin littafin ya amince da cewa Cif Mashood Abiola shi ne ya ci zaɓen da aka rushe a ranar 12 ga watan Yunin 1993.
“Lallai Mashood Abiola shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1993 bayan da ya samu ƙuri’u fiye da miliyan takwas inda ya samu nasara a kan Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC mai ƙuri’a fiye da miliyan biyar.” In ji Janar Babangida a cikin littafin da ya rubuta da kansa.