An yiwa masu matsalar gani 161 tiyatar Yanar Ido kyauta a babban asibitin Hadejia

0 58

Ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa ta ce masu matsalar gani 161 ne aka yiwa tiyatar Yanar Ido kyauta a babban asibitin Hadejia.

Babban jamiin kula da lafiyar Idanu na maaikatar lafiya ta jiha, Malam AU Abdulrahman ya sanar da hakan bayan kammala aikin.

AU Abdurrahman Umar ya ce an zabo masu matsalar idanun ne daga kananan hukumomin masarautar Hadejia.

Yana mai cewar gwamnatin jiha ta hannun maaikatar lafiya ta jiha suka dauki nauyin aikin tiyatar kyauta.

Ya bukaci wadanda aka yiwa aikin da su kiyaye da kaidoji da kuma dokokin da likitocin suka basu a lokacin tiyatar.

Malam AU Abdulrahman ya ce za a gudanar da irin wannan aiki kyauta a masarautar Kazaure a ranakun yau Litinin da kuma gobe talata A jawabansu da godiya wadanda aka yiwa aikin Idris Tela da kuma Binta Ibrahim Gawuna sun yabawa gwamnatin jiha bisa wannan karamci tare da alkawarin kiyayewa da dokokin da aka shimfida musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: