Gwamnatin jihar Jigawa ta aike da bahunhunan masara 990 domin rabawa al’ummar Karamar Hukumar Kazaure da aka hana fita na tsawon kwanaki 7 domin rage musu radadin zaman gida.
Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Jamilu Uwaisu Zaki ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse.
Yace bada bahunan masarar somin tabi ne daga gwamna Badaru Abubakar na tallafawa al’ummar dake zaune a gida.
Alhaji Jamilu Uwais Zaki yace a nata bangaren Karamar Hukumar Kazaure ta gudanar da feshi a muhimman wurare domin yaki da cutar corona.
Shugaban Karamar Hukumar ta Kazaure ya kara da cewa kwalejin kimiyya ta Hussain Adamu ta baiwa Karamar Hukumar gudunmawar sinadaren wankin hannu roba 300 domin tallafawa shirin yaki da cutar corona.