Mai Magana da yawun Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, ya ce harin da aka kai a Kwalejin koyar da aikin soja ta NDA a Kaduna na iya zama siyasa da kuma nufin kunyata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Manema Labarai sun rawaito cewa a ranar Talata ne wasu ƴan bindiga suka kai hari Kwalejin Sojoji da ke birnin Kaduna, kuma bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kashe sojoji biyu sannan suka sace soja guda ɗaya yayin harin da suka kai da tsakar dare.
Harin ya jawo hankalin yan Najeriya tare da haifar da damuwa kan karuwar matsalar tsaro a ƙasar.
Da yake mayar da martani kan harin a wata hira da gidan talabijin ta Channels a jiya Laraba, Malam Garba Shehu ya ce abubuwa da dama ka iya zama dalilan kai harin.
Haka Kuma Malam Garba Shehu ya ce Buhari ya yi Allah wadai da harin inda ya ce “wasu na iya kitsa harin domin kunyata gwamnatin Buhari saboda nasarorin da take samu a yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da kuma ƴan fashin daji.
Kazalika, ya ce bita da ƙullin siyasa na iya zama dalilin kai harin. Ya ce fadar shugaban kasar na sa ran sojoji za su yi bincike sosai domin gano abin da ya faru da dalilin faruwarsu tare da bayyana sakamakon bincikensu.