An yankewa matashi hukuncin daurin rai-da-rai saboda yi wa yarinya ’yar shekara 12 fyade
Babbar Kotun Jihar Jigawa dake nan Hadejia ta yanke wa wani mai suna Jibril Idi hukuncin daurin rai-da-rai saboda yi wa yarinya ’yar shekara 12 fyade da yi mata ciki.
Alkalin da ya zartar da hukuncin, Mai shari’a Ado Yusuf Birnin Kudu ya yankewa Idi hukunci ne bayan ya same shi da aikata laifin.
Jibril Idi ya yi wa yarinyar fyade tare da yi mata ciki a ranar 27 ga Mayun 2017, a kauyen Diginsa da ke karamar hukumar Birniwa ta Jihar Jigawa.
Wacce aka yiwa cikin, dalibar karamar makarantar sakandiren Diginsa ce ta garin Diginsa a karamar hukumar Birniwa.
A yayin shari’ar, wanda ake kara ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa da shi.
Lauyan masu gabatar da kara, ya gabatar da shaidu a gaban kotu.
Mai shari’a Ado Yusuf ya samu wanda ake tuhumar da aikata laifin fyade sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai don ya zama gargadi ga masu kokarin aikata hakan.