Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan amince wa wata tawagar manyan sojojin Nijeriya karkashin jagorancin Janar Christopher Musa, babban hafsan hafsoshin sojin Nijeriya (CDS) zuwa Jamhuriyar Nijar domin sake kulla zumuncin da ya tabarbare a tsakanin kasashen biyu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar, Farfesa Tanko Muhammad-Baba ya fitar ranar Lahadi a Kaduna.
A cewar ACF, ziyarar na nuni da samun sauyi mai kyau a alakar Nijeriya da Nijar da ta yi tsami a shekarar da ta gabata.
“ACF na kallon wannan huldar diflomasiyya a matsayin wani muhimmin mataki na maido da alakar ‘yan uwantaka mai tsawon tarihi da ke tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna a yammacin Afirka.”
ACF ta bayyana cewa, alaka dai tsakanin kasashen biyu ta tabarbare ne tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar a watan Yulin 2023.
Sanarwar ta ce, a martanin da ta mayar, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta dakatar da Nijar daga cikin mambobinta, tare da kakaba wasu jerin takunkumai, inda Nijeriya ke kan gaba wajen rufe iyakokinta, da sanya takunkumin tattalin arziki, da yanke muhimman kayayyakin more rayuwa zuwa kasar, da kuma yin barazanar daukar matakin soji a akan kasa