An yabawa gwamnan Jigawa kan amincewa da N500M domin magance matsalar karancin abinci mai gina jiki ga yara

0 268

An yabawa gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi, bisa amincewa da kudade tare da hadin guiwa da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF domin magance matsalar nkarancin abinci mai gina jiki ga yara masu fama da tamowa a.

Yabon na kunshe ne a cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, ai dauke da sa hannun babban jami’in yada labaran kungiyar, Ibrahim Isyaku, ya ce tallafin na naira miliyan 250 ga UNICEF shaida ce karara na gwamnatin jihar wajen cika alkawuran da ta dauka na magance dimbin kalubalen da mata da kananan yara ke fuskanta a jihar.

Sanarwar ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar amfani da kayan abinci yadda ya kamata da sauran abubuwan da suka dace.

Haka kuma ta yabawa hukumar UNICEF da sauran kungiyoyin raya kasa bisa tallafin da suke baiwa gwamnatin jihar tare da alkawarin yin taka tsan-tsan don ganin duk tallafin ya samu ga wadanda suka amfana.

Sawaba radio ta bayar da rahotan cewa gwamnatin jihar jigawa da asusun tallafawa kananan yar ana majalisaar dinkin duniya UNICEF sun amince da naira miliyan 500 domin magance karanci abinci tsakanin yara. Inda kusan yara dubu 10 zasu ci gajiyar shirin a jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: