An yabawa Gwamna Malam Umar Namadi dangane da gyara kasuwar kayan Gwari dake Guri

0 203

An yabawa Gwamna Malam Umar Namadi dangane da gyara kasuwar kayan Gwari dake Guri zuwa ta zamani.

Shugaban kasuwar kayan Gwari Alh Musa Zugo shine yayi wannan yabo yayinda yake yiwa manema labarai karin haske dangane da halin da kasuwar ke ciki musamman a wannan lokaci.

Shugaban kasuwar yace Gwamnan Malam Umar ya nuna kudirin sa na sabunta kasuwar la’kari da yadda ‘Yan kasuwa daga Kaduncin kasar nan ke zuwa domin siyasa danyen kaya musamman danyen Attaruhu.

Yace a duk karshen Damina da kuma lokacin sanyi karamar hukumar Guri na samar da danyen Attaruhu, wanda ya kasance mutanen kudancin kasar nan suna sun shi matuka.

Ya kara da cewa, kasuwar Gwari ta Guri na fitar da daruruwan motocin danyan kayan miya.

Amma ya bayyana cewa, a wannan lokacin kasuwar na fuskantar tarin matsaloli kamar ruwan sama da rashin rumfuna da kuma karancin wuraran ajiye ababan hawa. Shugaban kasuwar ya kara da cewa, kasuwar na tara kudaden shiga masu yawa a kullum ga karamar hukumar dama Jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: