An ware ₦100Bn a cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin shirin ciyar da dalibai yan makaranta

0 287

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 100 a cikin kasafin kudin shekarar 2024 domin shirin ciyar da dalibai yan makaranta.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin rattaba hannu kan kudirin kasafin kudi na shekarar 2024 da ya zama doka a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa, wannan tanadin zai zama abin karawa dalibai kwarin gwiwa wajen halartar makarantu da kuma rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta. A farkon watan Disambar bara,Shugaban kasar ya ba da umarnin sake dawo da shirin ciyar da dalibai a makarantu tare da ba da umarnin sauya tsarin daga ma’aikatar jin kai zuwa ma’aikatar ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: