An umarci miliyoyin mutane su yi ƙaura daga gidajensu gabanin isowar guguwar milton a Amurka

0 197

An umarci miliyoyin mutane su yi ƙaura daga gidajensu a daidai lokacin da guguwar milton take gab da isowa yammacin gaɓar Florida.

Ana tunanin wannan guguwar wadda ta kai mataki na biyar, mai ɗauke da iska mai ƙarfi, za ta kasance guguwa mafi ƙarfi da ta auku a yankin na Amurka.

A daren jiya, shugaban Amurka, Joe Biden ya yi gargaɗi ga mutanen yankin su yi ƙaura, inda ya ce, “ku tashi daga yankin,” kamar yadda ya shaida wa mutanen Florida.

Fargabar guguwar ta janyo ƙaura mafi girma a cikin shekaru, inda gwamnan jihar Ron DeSantis shi ma ya yi gargaɗin cewa guguwar ta kusa.

Wannan guguwa na zuwa ne kimanin mako biyu bayan guguwar Helene – wadda ta kashe aƙalla mutane 224, sannan ɗaruruwa suka ɓace a ƙasar ta Amurka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: