An tsawaita rajistar takardar lasisin harkokin man fetur na shekarar 2024 da kwanaki 10

0 153

Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta kasa NUPRC, ta sanar da tsawaita rajistar takardar lasisin 2024 da kwanaki 10.

Babban Jami’in Hukumar, Engr. Gbenga Komolafe, wanda ya bayyana hakan jiya Talata a Abuja, ya ce an kara wa’adin ne domin baiwa masu sha’awar zuba jari damar cin gajiyar wannan damammakin.

Komolafe ya bayyana cewa, hukumar ta yi aiki tukuru tare da kamfanoni masu zaman kansu, domin kara gudanar da ayyukan bincike da kara karfafa gwiwar masu zuba jari. 

A wajen taron, Komolafe ya nanata aniyar Najeriya na ci gaba da bunkasa fannin mai da iskar gas, sannan ya bayyana irin kwarin gwiwar da jagorancin shugaba Bola Tinubu ya yi da nufin jawo hankalin masu zuba jari na kasa da kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: