An tsare wani mataimakin ministan tsaron kasar Rasha bisa zargin karbar cin hanci

0 251

Timur Ivanov, wanda ke rike da mukamin tun shekara ta 2016, an tsare shi, in ji kwamitin binciken Rasha ba tare da bayar da wani karin bayani ba.

Kamfanin dillancin labarai na TASS ya ruwaito cewa ana zarginsa da karbar cin hancin da ya kai akalla dalar Amurka dubu 10 kuma zai iya fuskantar daurin shekaru 15 a gidan yari idan aka same shi da laifin.

Ivanov wanda ke da alhakin kula da ayyukan gine-gine karkashin ma’aikatar tsaro, ciki har da yankunan Ukraine da Rasha ta lalata tare da mamaye su.

An zargi Ivanov kan cin hanci da rashawa bayan mamayar da Rasha ta yi a Ukraine a watan Fabrairun 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: