Jami’an hakumar shige da ficin a Burtaniya sun tsare dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi a birnin Landan inda ya yi bikin Easter.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin yada labaransa Obi-Datti Diran Onifade ya fitar a cikin wata sanarwa a jiya, inda ya ce Obi ya fuskanci cin zarafi daga jami’an shige da fice na Landan.
A cewarsa, dan takarar shugaban kasa na jamiyyar Labour a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Fabrairu ya isa filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan daga Najeriya a ranar Juma’a, 7 ga Afrilu, kuma ya layin cika wajiban ka’idojin filin jirgi a lokacin da jami’in shige-da-fice suka kamashi.
Onifade ya kuma kara da cewa, Obi na fuskantar matsin lamba, tun bayan zaben shugaban kasa da aka yi a watan Fabrairu inda ya nuna bajintar ya zo na uku cikin yan takarar shugaban kasa 18 kamar yadda INEC ta sanar.