Kwamitin tara kudaden shiga na karamar hukumar Kafin Hausa ya tara kudaden shiga sama da naira miliyan goma sha biyar daga manyan kasuwanni hudu a cikin makwanni goma sha hudu da suka gabata.
Shugaban kwamitin, Idrith A. Sabo Cashier, ya bayyana hakan ga manema labarai bayan mika rahoton kwamitin ga karamar hukumar.
Ya ce kafin kafa wannan kwamiti, ana samun harajin naira dubu tamanin kacal a kowane mako amma bayan kafa kwamitin an samu karin kudin shiga zuwa naira dubu dari bakwai a kowane mako.
Shugaban kwamitin ya tabbatar wa jama’a cewa za a yi amfani da wadannan kudade wajen samar da kayayyakin more rayuwa a kasuwannin domin amfanin al’umma.
Ya yi kira ga jama’a da su guji yin bahaya a fili a kusa da kasuwanni domin kare kai daga kamuwa da cututtuka, wanda ya yi daidai da manufofin gwamnatin Jihar Jigawa na kawo karshen yin bahaya a fili.