An tabbatar da mutuwar wasu mutum uku sakamakon fashewar gas ɗin girki a Nairobi

0 261

Mutum uku aka tabbatar da mutuwarsu yayin da sama da 300 suka jikkata sakamakon wata mummunar fashewar gas ɗin girki a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya.

Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya ce wata babbar mota ce ɗauke da tukwanen gas ta fashe a unguwar Embakasi a daren jiya, lamarin da ya haddasa tashin gobara a yankin.

Hotunan bidiyon a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wuta da hayaƙi suka turnuƙe saman rukunin benaye yayin da mutane suka shiga firgici da ruɗani domin neman tsira.

Gidaje da kasuwanni, da shaguna da motoci dama ne suka ƙone sakamakon tashin gobarar.

Tun da farko, gwamnatin ƙasar ta ce fashewar ta auku ne a cibiyar sayar da gas ɗin, sai dai kawo yanzu ba a san abin da haddasa fashewar ba.

Mazauna yankin Embakasi da ke kudu maso gabashin Nairobi sun ce sun ji kamar girgiza kafin ganin haske a sama a tsakar dare.

Da yawa daga cikin waɗanda suka jikkata an ce sun shaƙi hayaƙi ne, ciki har da ƙananan yara 25, kamar tadda wata kafar yaɗa labarai a ƙasar ta ruwaito. Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce ta kai mutum 271 da suka samu munanan raunuka zuwa babban asibitin ƙasar da ke Nairobi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: