An shigar da marasa galihu 124,000 cikin tsarin kiwon lafiya a jihar Borno
Gwamnatin jihar Borno ta ce ta shigar da marasa galihu 124,000 da ‘yan tada kayar baya suka shiga cikin tsarin kiwon lafiya a wasu kananan hukumomin jihar.
Sakataren zartarwa na Hukumar Bada Agajin Lafiya ta Jihar Borno Dokta Saleh Abba ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Maiduguri, inda ya ce hukumar na da niyyar daukar marasa galihu 250,000.
Ya jaddada cewa shirin ya ba da fifiko ga zaman lafiya ta hanyar tabbatar da cewa kowace Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) ta sami kudaden da suka dace daidai da bukatunsu na musamman, a cikin mawuyacin hali don isa ga al’ummomin tafkin Chadi. Ya ce sun shigar da marasa galihu da suka hada da mata masu juna biyu da yara da tsoffi da kuma nakasassu cikin shirin kiwon lafiya kyauta.