An samu ‘yan takara 20 da laifin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar Kano

0 110

Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Najeriya ta ce ta samu ‘yan takarar shugabannin ƙananan hukumomin Kano 20 da laifin ta’ammali da ƙwaya bayan gwajin ƙwayoyin da aka yi musu.

Jaridar daily Trust ta ambato shugaban hukumar NDLEA na jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, na cewa gwaji ya tabbatar da cewa wasu daga cikin ‘yan takarar – waɗanda jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar ta gabatar – an same su da laifin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Ya ƙara da cewa hukumar na sa ra san kammala aikin tantance ‘yan takarar ta hanyar gwajin ƙwayar kafin wa’adin da aka ɗibar mata na kammala aikin.

Jam’iyyar NNPP ce dai ta buƙaci a yi wa duka ‘yan takarar shugabannin ƙananan hukumomin gwajin a wani abu da wasu ke kallo a matsayin matakin rage yawan ‘yan takarar.

Hukumar zaɓen jihar dai ta sanya ranar 26 ga watan Ocotober domin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin jihar 44 haɗe da kansiloli a mazaɓu 484.

Leave a Reply

%d bloggers like this: