A jiya Talata rundunar sojojin Najeriya ta sanar da tashin gobara a helkwatarta dake babban birnin kasar Abuja, amma ba a samu hasarar rayuka ba.
Kakakin hukumar sojojin kasar ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, matsalar lantarki ne ta haddasa tashin gobarar a ginin hukumar.
Mohammed Yerima, kakakin rundunar sojojin Najeriya ya ce, wasu wayoyin lantarki ne suka haifar da gobarar a ginin helkwatar sojojin kasar da safiyar wannan rana. Ya ce lamarin ya faru ne a sanadiyyar lalacewar wayar lantarki a wani ofishin dake ginin hukumar.
Jami’in ya ce, ma’aikatan kwana-kwana sun yi nasarar kashe wutar cikin kankanin lokaci, ko da yake da ma ana gudanar da aikin gyare gyare a helkwatar wanda ya hada har da aikin gyaran wayoyin lantarki.