An samu tabbacin tsammanin albarkatun danyen mai a jihar Jigawa

0 355

Hukumar tara haraji da rabon arzikin kasa ta tabbatar da samun albarkatun man fetir daya ratso daga kasar Libya zuwa kananan hukumomin Maigatari da Babura a nan jihar Jigawa.

Kwamishinan hukumar na kasa Ahmed Mahmud Gumel ya sanar da hakan ta wani shirin Radio Jigawa.

Yace a yanzu haka gwamnatin tarayya zata fara hako albarkatun man da ya ratso jihar Jigawa.

Ahmed Mahmud ya kara da cewa an samu rijiyoyin man fetir a jihoshin Gombe da Bauchi wadanda tuni aka kammala safiyon aikin fara hako man.

Kwamishinan hukumar rabon arzikin kasar wanda kuma shine tsohan mataimakin gwamnan jihar Jigawa yace Allah ya albarkaci yankin Arewa da albarkatun kasa da suka hada da man fetir da ma’adinai.

Ahmed Mahmud ya yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari da gwamna Muhammadu Badaru Abubakar bisa kudirorinsu na bunkasa tattalin jihar Jigawa da ma kasa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: