An Samu Karancin Fitowar Masu Zabe A Jihar Ribas

0 171

An samu karancin fitowar masu zabe a zaben ciki gibi na dan majalisar tarayya mai wakilai mazabar Fatakwal a jihar Rivers.
Sai dai, akwai zaman lafiya a wajen zaben inda ake da ‘yansanda da jami’in hukumar civil defense a guraren kada kuri’a.
A wani lamarin makamancin wannan, an samu karancin fitowar masu zabe a zaben ciki gibi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya a jihar Ebonyi.
An gudanar da zaben cike gibin a wasu mazabu dake kananan hukumar 7 wadanda lamarin ya shafa a jihar ta Ebonyi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana zabukan a matsayin wadanda ba su kammalu ba a yankunan saboda tashin hankali da sauran matsaloli.
Wasu daga cikin masu zabe, wadanda suka zanta da kamfanin dillancin labarai na kasa, sun danganta karancin fitowar masu zabe da kokonto kan yadda ake gudanar da zabukan wadanda ya kamata su zama bisa gaskiya da adalchi.

Leave a Reply