An tsinci gawar ɗan majalisar jihar Anambra, Justice Azuka mai wakiltar ƙaramar hukumar Onitsha ta Arewa, gunduma ta farko.
Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa haɗin gwiwar jami’asn tsaron ƙasar ne suka gano gawar a gadar 2nd Niger Bridge.
A watan Disamban da ya gabata ne aka sace ɗan majalisar a birnin Onitsha.
Bayan shafe makonni ana bincike jami’an tsaro daga Abuja, suka kama wasu mutane da ake zargi da sace ɗan majalisar, inda suka kai jami’an har inda suka jefar da gawar Mista Azuka.
Wannan shi ne karo na biyu da ake sace ɗan majalisar jihar Anambra kuma a kashe shi a shekarun baya-bayan nan.
A shekarar 2022 ma an sace wani ɗan majalisa mai suna Okey Okoye, inda daga baya kuma aka kashe shi a wani yanki na jihar.