An samu ƙarin masu Korona 2 a Jigawa, Gwamna Badaru ya dauki Sabbin matakai

0 404

An samu masu ƙarin masu Korona a Jigawa Gwamna Badaru Muhammad ya dauki Sabbin matakai. Ga kadan daga cikin jawabinsa a Daren Yau.

1- Sakamakon samun sabbin masu ɗauke da cutar Korona a Gujungu a ƙaramar Hukumar Taura da Wani Ɗan ƙaramar Hukumar Birnin Kudu Mai aiki a Gumel, za a kulle Gumel da Gujungu da kuma Birnin Kudu domin a bibiyi waɗanda suka yi mu’amala da masu ɗauke da cutar don yi musu gwaji.

2- Kullewar ta Mako guda ce Kacal farawa daga ranar Alhamis 31/04/2020 da karfe 12:00am (Dare)

3- Mutane biyun da aka samu tun asali ɗaya da aka kawo daga Kano da kuma wanda aka samu a Kazaure duk suna murmurewa

4- A Jigawa kawo yanzu mutane biyu ne aka tabbatar da kamuwarsu har da sabbin biyun nan sun zama 4 kenan, yayin da ana kan dudduba mutane 398, an yiwa mutane 58 gwaji ana jiran sakamako.

5- Mutane 16 Daga cikin mutane 17 da aka gwada a Kazaure ba su dauke da cutar. Bayan Fitowar sakamakon mutum ɗayan ana sa ran janye dokar zaman gida a yankin Kazaure.

Leave a Reply

%d bloggers like this: