An sallami Firayim Ministan Isra’ila daga asibiti bayan tiyatar da aka yi masa a zuciya

0 298

An sallami Firayim Ministan Isra’ila Benjamin daga asibiti a safiyar yau bayan tiyatar da aka yi masa a zuciya.

Hakan dai ya faru ne sa’o’i kadan gabanin kada kuri’ar da majalisar dokokin kasar ta kada kan sauye-sauyen da ya ke shirin yi na shari’a.

Mai magana da yawun Shugaban yace Netanyahu ya bar asibitin Sheba da ke kusa da Tel Aviv.

An sa masa na’urar bugun zuciya (karamar na’urar da ke da batir da ke hana zuciya bugawa a hankali) a karshen mako.

Sallamar  Netanyahu ta zo ne gabanin kada kuri’a mai mahimmanci kan wani muhimmin bangare na sake fasalin shari’arsa mai raba kan jama’a, wanda aka shirya yi a yau Litinin a majalisar dokokin Isra’ila a birnin Kudus. Yayin da yake kwance a asibiti, firaministan ya gana da madugun ‘yan adawa Yair Lapid a wani bangare na kokarin da shugaba Isaac Herzog ke yi na cimma matsaya na karshe kafin kada kuri’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: