An sako ɗalibai da malaman makarantar ‘Apostolic Faith Montessori’ da ke jihar Ekiti

0 194

An sako ɗalibai da malaman makarantar ‘Apostolic Faith Montessori’ da ke jihar Ekiti da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Litinin da ta gabata.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Sunday Abutu, ya tabbatar da sakin ɗaliban tare da malamansu cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Sai dai kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce maharan sun kashe direban motar ɗaliban a lokacin da suke hannunsu.

An dai sace ɗaliban da malaman nasu ne a lokacin da suke dawowa daga wata tafiya da suka yi.

Dalibai biyar ne da malamansu uku da kuma direban motar ne ke cikin motar a lokacin da aka sace su.

Sun kuma shafe kusan kwanaki bakwai a hannun ‘yan bindigar da suka sace su.

Cikin wata sanarwar da ta fitar, gwamnatin jihar ta tabbatar da sakin ɗaliban tare da malamansu.

Sanarwar ta kuma ambato gwamnan jihar Biodun Oyebanji na gode wa shugaban ƙasar Bola Tinubu kan goyon bayan da ya bayar wanda shi ne ya taimaka har aka kai ga sakin mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: